Hausa360
Media Company
Hausa360 Ingantaccen shafi domin Hausawa a fadin duniya, Muna yada muku rohotani da labarai na Nishadi, Al'adu, Siyasa, Ilmantarwa, Addini, Wasanni da sauran su a zamanan ce. Source
Actions
Media Outlet details
| Scope | International |
|---|---|
| Language | Hausa |
| Country | Nigeria |
|
Similarweb UVM |
Request pricing |
|
Comscore UVM |
Request pricing |
Recent Articles
Search ArticlesKotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kashe Amarya A Farawa
Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 22 ta yanke wa wani matashi, Shu’aibu Abdulkadir, hukuncin kisa bayan samunsa da laifin kashe amarya Rumasa’u a gidanta da ke Farawa a Jihar Kano. Mai Shari’a Farida Dan Baffa ce ta yanke hukuncin bayan ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati ya gabatar. Lamarin dai ya faru ne a shekarar 2025, lokacin da Shu’aibu ya je gidan marigayiya Rumasa’u da ke Farawa. An zarge shi da kashe ta bayan ta sanar da shi cewa tana dauke da juna biyunsa shi ya mata ciki.
Matsaloli 7 Da Yawan Shan Soft Drinks Ke Jawowa
Yawan shan soft drinks da energy drinks kamar Coke da Fearless na iya janyo matsalolin lafiya masu yawa. Wadannan abubuwan sha suna dauke da sinadarai masu cutarwa ga jiki idan aka sha su da yawa. A nan ne wasu matsaloli guda bakwai da yawan shan su ke iya jawowa. Yawan shan wadannan abubuwan sha na iya kara hadarin ciwon suga (Type 2 Diabetes). Wannan saboda yawan sukarin da ke cikinsu yana sa jiki ya kasa sarrafa sukarin jini yadda ya kamata. Suna jawo kiba da taruwar kitse a jiki.
Saudiyya Ta Yi Allah-Wadai Da Hare-haren Iran
Saudi Arebiya ta yi Allah-wadai da hare-haren da Iran ke ci gaba da kai wa kasashen Kuwait, Bahrain, da Jordan. Ma’aikatar Harkokin Waje ta Saudiyya ta bayyana cewa tana goyon bayan kasashen da abin ya shafa. Wannan ya zo ne a yayin da ake fama da rikici tsakanin Iran da Amurka a kan mashigar ruwan Hormuz. Kuwait da Bahrain sun fuskanci hare-haren sama daga Iran a ranar Alhamis. Jordan kuma an kai mata hari a kwanakin baya.
Hausa360 Ta Kaddamar Da Sabon Logo, Za Ta Fara Shirya Fina-Finai
Hausa360, dandalin yada labarai na zamani, ta kaddamar da sabon tambarin a hukumance. Babban Daraktan Fasaha da Ayyuka na kamfanin, Yahaya Shuaibu Musa, ne ya sanar da hakan a watan Yuni, 2026. Ya kuma bayyana shirin kamfanin na fadada ayyukanta ta hanyar shiga harkar samar da fina-finai da watsa shirye-shirye. Wannan sabon tambari ya maye gurbin tsohon tambarin kamfanin. Yana dauke da sabon salo na zamani wanda ke wakiltar cigaba da inganci.
Sanata Shehu Buba Ya Ci Gaba Da Raba Keken Ga Mata
Sanata Shehu Buba Umar ya ci gaba da raba kekunan NAPEP ga matan da suka ba shi goyon baya a tafiyarsa ta siyasa. Babban hadiminsa, Salim Yahaya Yaro, ya kai ziyara Gundumar Makama B inda ya miƙa kekunan NAPEP guda huɗu ga mata. Wannan tallafi na nuna jajircewar Sanatan wajen inganta rayuwar al’umma. Salim Yahaya Yaro ne ya jagoranci rabon kekunan a Gundumar Makama B. Ya miƙa kekunan guda ɗaya-ɗaya ga mata huɗu da suka marawa Sanata baya.
KASEDA Ta Gayyato Yan Kasuwa Zuwa Taron Wayar Da Kai
Hukumar Kula da Habbaka Kananan Sana’oi ta Jihar Katsina (KASEDA) ta gayyaci dukkan kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, kungiyoyinsu, matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki zuwa taron wayar da kai da tattaunawa. Taron zai mayar da hankali kan ci gaba da farfado da Kanana da Matsakaitan Masana’antu (MSMEs) a jihar Katsina. A yayin taron, za a tattauna hanyoyin bunkasa kasuwanci da ci gaban kanana da matsakaitan masana’antu.
An Kashe Mai Gadin Asibiti A Warawa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad Barayi sun kashe Malam Ado Shu’aibu Maki, mai gadin asibiti a mazaɓar Danlasan. Sun yi masa kisan gilla ta hanyar yankan rago a daren Juma’a, 3 ga Yuli, 2026. Sun kuma sace kayan sola da ke asibitin da yake a Ƙaramar Hukumar Warawa, Jihar Kano. Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Shugaban Ƙaramar Hukumar Warawa, Malam Hamza Kinchau, ya fitar a ranar Asabar, 4 ga Yuli, 2026.
Jasawa sun koka Koka Kan Rashin Jasawa A Mukamai
Abdulrahman Ismail ya koka kan yadda al’ummar Jasawa ba su samu mukamai masu yawa a gwamnatin tarayya ba. Ya ce duk da akwai mukamai sama da 700 da ke karkashin gwamnatin tarayya, har yanzu ba a bai wa Jasawa ko daya ko biyu ba. Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Abdulrahman Ismail ya kawo misalin manyan hukumomi 100 da shugaban kasa ke nada shugabanninsu.
BellBank Ta Kai Karar CBN Kan Soke Lasisi
BellBank ta kalubalanci matakin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauka na soke lasisin ta. A cikin wata sanarwa, wanda ya kafa bankin, Bello Kano, ya ce bankin bai yarda da dalilan da hukumar ta bayar ba. Bankin ya fara shigar da karar a hukumance. A cikin sakon da aka aika wa abokan hulda, BellBank ta tabbatar wa abokan cinikinta cewa tana daukar matakin shari’a.
ATBU Ta Soke Bayar Da Fili Ga Daliban Tijjaniyya
Hukumar Gudanarwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta sanar da soke shirin bai wa kungiyar daliban darikar Tijjaniyya fili a harabar jami’ar. An kuma umarci dukkannin mabiya dariku da sauran al’ummar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadunsu a babban masallacin jami’ar ba tare da wani nau’in tsangwama ba.