Karanta rubutu kawai domin rage cin data Asalin hoton, Getty Images Bayani kan maƙala Marubuci, Lucy Sherriff Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future Mintuna 3 da suka wuce Lokacin karatu: Minti 5 Shekaru aru-aru da suka shuɗe, mata a faɗin duniya sukan haihu ne a tsaye - ko su durƙusa a gwiwoyinsu, ta hanyar amfani da kujera, ko su tsuguna. Ana ganin ma durƙusawa yayin naƙuda na iya ƙara faɗin ƙashin ƙugu da aƙalla santimita 2.5cm, kuma hakan yana sa a samu sauƙin haihuwa.