4 awanni baya Mesut Ozil, wani ɗan wasa ne da ba za a manta da shi a tarihi, musamman a zukatan masoya Real Madrid da Arsenal, da ma wasu ƙungiyoyi a Jamus da Turkiyya. An haifi Mesut Ozil a birnin Gelsenkirchen na Jamus, kuma iyayensa Turkawa ne mazauna Jamus. Kakansa Baturke ne da ya je ƙwadago Jamus ta Yamma, wanda ya sa Ozil ke yawan ambaton tushensa na Turkiyya.