Takardun kotu sun zargi tsohon Akanta Janar na Bauchi, Dakta Sa’idu Abubakar, da karkatar da kusan Naira biliyan 40 da sunan rance Ana zarginsa da amfani da sunan gwamnatin Bauchi wajen neman rance don kwangilolin babura da ake cewa ba a gani a ƙasa ba Gwamnatin jihar ta shigar da tuhume-tuhume 16 da suka haɗa da zamba, ƙirƙirar takardun bogi, cin amanar aiki da karkatar da kuɗaɗin talakawa A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit.